16 Satumba 2025 - 21:30
Source: ABNA24
Isra'ila Ta Kai Hare-Hare 12 A Yamen + Bidiyo 

Majiyar Yaman: Ya zuwa yanzu Isra'ila ta kai hare-hare 12 kan tashoshi 3 da ke tashar jiragen ruwa na Hodeidah sannan an kai wasu harin bama-bamai a birnin Hodeidah.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Birgediya Janar Yahya Saree, kakakin rundunar sojin Yaman ya tabbatar da cewa A halin yanzu, tsaron sararin samaniyar mu na fuskantar jiragen Isra'ila da ke kai hare-haren ta'addanci ga Yemen.

Na'urorin tsaron kariyar sararin samaniyar Yamen ya haifar da rudani sosai tsakanin jiragen makiya tare da tilastawa wasu jiragen yakin barin sararin samaniyar kafin su kai harin. Cikin ikon Allah an dakile shigarsu cikin kasar.

Sojojin Isra'ila a basu bayanin sun ce: Harin da aka kai a tashar jiragen ruwa na Hodeidah martani ne ga hare-haren da Yamen ta ke kaiwa lokacin zuwa lokaci ga Isra'ila na hari da jirage marasa matuka da makamai masu linzami.

Kafin nan Sojojin Isra'ila sun fitar da sanarwar cewar nan da sa'o'i masu zuwa za su kai hari tashar jiragen ruwa ta Hodeidah ta Yaman.

Lokaci ɗaya da fara kai harin kasa da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai keyi a Gaza, Tel Aviv ta ba da sanarwar ficewar gaggawa ga mazauna tashar jiragen ruwa na Hodeidah a kasar Yemen. Tun da farko dai hare-haren da Isra'ila ta kai a Sanaa da Al-Jawf ya janyo asarar rayukan 'yan jarida da jami'an kasar Yemen da dama. Sojojin na Yaman kuwa suna ta amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuka wajen kaiwa Isra'ila hari a yunkurinsu na tallafawa al'ummar Gaza.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha